Tunisia - 'Yan Ci Rani

'Yan ci rani 23 sun bace a gabar ruwan Tunisia

Wani jami'in tsaron gabar ruwan Tunisia
Wani jami'in tsaron gabar ruwan Tunisia FETHI BELAID / AFP

Kungiyar agaji ta Red Crescent ta ce ‘yan ci rani 23 suka bata, yayin wasu biyu suka mutu a gabar ruwan Tunisia sakamakon kifewar da kwale kwalen dake dauke da mutane sama da 100 yayi.

Talla

Rundunar sojin ruwan Tunisia tace kwale kwalen da ya tashi daga gabar ruwan Zuwara na kan hanyar zuwa Turai kafin karo da sojoji kusa da tashar man Miskar.

Sojojin sun ce sun mika sauran bakin ga kungiyar dake kula da kaurar baki da suka kunshi Yan kasar Eritrea 37 da Yan kasar Sudan 32 da dan kasar Masar guda, kuma dukkansu suna tsakanin shekara 15 zuwa 40.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.