Daruruwan mutane sun yi zanga zanga a Mali

Kanar Assimi Goïta shugaban mulkin sojin Mali
Kanar Assimi Goïta shugaban mulkin sojin Mali AP

Magoya bayan Yan adawar Mali da ake kira M5 sun gudanar da zanga zanga a birnin Bamako yayin da suke shirin karbar mukamai domin shiga gwamnatin sojin kasar bayan mulkin da sojoji suka sake gudanarwa

Talla

Kamfanin dillancin labaran Faransa yace daruruwan magoya bayan Yan adawar ne suka yi gangami a Dandalin dake tsakiyar birnin Bamako domin tuna lokacin da aka kafa kungiyar bara wadda ta haifar da mummunar zanga zanga goyan bayan sojin da suka yi juyin mulki.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kasar Faransa ta sanar da dakatar da aikin soji tare da Mali saboda juyin mulkin.

Abdoulaye Cisse wani matashi dake goyan bayan Yan adawar ya bukaci Mali da ta nemi sabbin kawaye saboda sanarwar da Faransa tayi, yayin da Kalou Sow, wani ma’aikacin gwamnati ya bukaci al’ummar kasar da su yabawa Faransa saboda rawar da take takawa a kasar.

Rahotanni sun ce shugaban sojin Assimi Goita na tunanin nada wani daga bangaren M5 a matsayin sabon Firaminista abinda ake ganin zai kwantar da hankalin kasashen duniya.

Gwamnatin Faransa tace dakatar da aiki da sojin Mali na wucin gadi ne har zuwa lokacin da gwamnatin sojin kasar zata tabbatar musu da shirin gudanar da zabe a watan Fabarairun shekarar 2022.

Faransa na da dakaru 5,100 a karkashin rundunar Barkhane dake yaki da Yan ta’adda a yankin Sahel wadanda suka hada da jiragen yaki da jiragen dake sarrafa kan su a birnin Yammai dake Jamhuriyar Nijar.

Kakakin rundunar sojin Faransa Frederic Barbry ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar duk da daukar matakin da suka yi na dakatar da aiki tare da sojin Mali zasu cigaba da kai hare hare kann yan ta’adda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.