Chadi

CEEAC ta bukaci Chadi ta mika mulki ga fararen hula

Shugaban gwamnatin sojin Chadi Janar Mahamat Idriss Déby Itno yayin jana'izar mahaifinsa Idris Déby Itno, Ranar 23 ga watan Afriluin shekarar 2021
Shugaban gwamnatin sojin Chadi Janar Mahamat Idriss Déby Itno yayin jana'izar mahaifinsa Idris Déby Itno, Ranar 23 ga watan Afriluin shekarar 2021 REUTERS - STRINGER

Shugabannin kasashen yankin Tsakiyar Afirka da ke ganawa a Kwango, sun bukaci hukumomin sojin Chadi da su mika Mulki ga fararen hula cikin watanni 18 masu zuwa.

Talla

Gwamnatin mulkin sojan Chadi ta fara aiki ne a ranar 20 ga watan Afrilu bayan da Shugaba Idriss Deby Itno, da ya shugabancin Chadi na shekaru 30, ya rasu yayin fafatawa da ‘yan tawaye.

Dan shugaban Deby,  Mahamat, janar din soja mai tauraru huɗu, ya bayyana kansa a matsayin shugaban ƙasa bayan mutuwar mahaifinsa.

Shugabannin kasashen CEEAC

Yayin taron na ranar Jumma’a a Brazzaville shugabannin kasashen Angola da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Congo da Jamhuriyar Demokradiyyar Congo sun bukaci shugabannin mulkin soja da su shirya "tattaunawa ta kasa baki daya cikin ba tare da bata lokaci ba.

A bayanansu na karshe bayan taron kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Tsakiyar Afirka (CEEAC), sun yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a siyasar kasar "don cimma burin mika Mulki ga fararen hula cikin watanni 18".

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.