Mali-Ta'addanci

'Yan ta'adda sun kashe fararen hula 11 a Mali

Shugaban gwamnatin soji Mali, Assimi Goita,
Shugaban gwamnatin soji Mali, Assimi Goita, © Nipah Dennis / AFP

Akalla fararen hula Azbinawa 11 aka kashe kusa da garin Menaka da ke arewacin Mali da ke fama da rikici, kamar yadda kungiyar dakarun kawance da ke goyon bayan gwamnati ta sanar a jiya Asabar.

Talla

Kungiyar ta ce  wasu mahara da ba a shaida sub a ne suka kai hari a garin Agharangabo, inda suka aikata ta’asa.

Agharangabo da Menaka na daga cikin makeken yankin da aka amannar cewa gwamnati ba ta da iko a kan su kasar ta Mali, sakamAkon cewa su na karkashin ikon mayaka masu ikirarin jihadi.

 Tun a shekarar 2021 ne yankin ke fama da hare hare daga mayaka masu ikirarin jihadi, da kuma munanan rikice rikice tsakanin al’umomi dabam dabam da ke zaune a yankin.

Rahotanni sun ce maharani sun yi awon gaba da dabbobin mutane 11 da suka kashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.