Afrika-Coronavirus

Gidauniyar Mastercard za ta karfafa aikin rigakafin corona a Afrika

Wani bangare na aikin fadada rigakafi ga Afrikawa da gidauniyar ta Mastercard ke kan yi yanzu haka.
Wani bangare na aikin fadada rigakafi ga Afrikawa da gidauniyar ta Mastercard ke kan yi yanzu haka. Michele Spatari AFP/File

Gidauniyar Mastercard ta sanar da ware dala biliyan daya da miliyan dari uku domin wayar da kai game da allurar rigakafin coronavirus a nahiyar Afirka, tare da hadin gwiwar cibiyoyihn dakile cutuka masu yaduwa da ke nahiyar.

Talla

Sanarwar hadin gwiwa tsakanin gidauniyar da kuma cibiyar dakile cutuka masu yaduwa ta Afirka, ta ce za a samar da alluran rigakafi ga akalla mutane miliyan hamsin da kuma zuba jari ta yadda za a samu wadatuwar alluran.

Gidauniyar ta ce an shirya gangamin ne, domin tallafawa tarayyar Afirka cimma  kashi sittin cikin dari na allurar rigakafin ga al’ummar yankin daga nan zuwa karshen shekarar 2022.

Kawo yanzu dai kasa da kashi biyu cikin dari na ‘yan Afirka ne suka karbi allurar rigakafin cutar ta corona.

A makon da ya wuce ne Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa Nahiyar Afirka bata daukar matakan da suka dace na yaki da cutar ta fuskar rigakafi bayan samun raguwar allurar rigakafin cutar, da kuma rashin ingatattun kayayyakin kiwon lafiya, idan aka kwatanta da kasashe masu karfin tattalin arziki.

Shugaban cibiyar yaki da cutuka masu yaduwa ta Afrika John Nkengasong ya ce gidauniyar ta shirya taimakawa nahiyar ta yadda za ta wadatu da rigakafin don samun nasarar yakar cutar.

A bangare guda shugaban gidauniyar ta Mastercard Reeta Roy, matakin na su ya biyo bayan tangardar da suka fuskanci nahiyar Afrika na da shi ta fuskar yaki da covid-19 da kuma fafutukar da ta ke wajen ceto al'ummarta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI