Sudan

Janye tallafin bangaren man fetur a Sudan ya haddasa tashin farashi

Wasu masu zanga-zanga a Sudan.
Wasu masu zanga-zanga a Sudan. © RFI/Laura-Angela Bagnetto

Gwamnatin Sudan ta kammala janye ilahirin tallafin man fetur da dizel wanda ta ke shigarwa daga ketare, matakin da ya ninka farashinsu sabanin yadda aka saba saye.

Talla

Rahotanni sun ce yanzu haka farashin man fetur da al’ummar ta Sudan suka saba saye kan fam 150 ya koma 290 yayinda farashin dizel ya koma fam 285 daga 125 da ake saye a baya.

Ma’aikatar kudin kasar da ke sanar da matakin, ta ce Sudan na kashe biliyoyin daloli wajen biyan tallafin kowacce shekara.

Ko a baya tashin farashin man ya haddasa zazzafar zanga-zanga a sassan kasar.

Garambawul ga tsarin tattalin arzikin kasar ne dai ya kai ga hambarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Omar al-Bashir bayan tashin goron zabbin da farashin kayaki ya yi a sassan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.