Mali - Siyasa

Sojojin Mali sun tabbatarwa ECOWAS alkawarin mikawa farar hula mulki

Kanal Assimi Goita shugaban gwamnatin sojojin Mali.
Kanal Assimi Goita shugaban gwamnatin sojojin Mali. MALIK KONATE AFP/File

Shugaban Kungiyar kasashen Afirka ta Yamma Jean-Claude Kassi Brou yace hukumomin kasar Mali sun tabbatar da aniyar su ta dawo da mulkin dimokiradiya a cikin kasar.

Talla

Brou wanda ke cikin tawagar wakilan kungiyar ECOWAS da ta ziyarci Bamako bayan Kanar Assimi Goita ya karbe iko daga hannun gwamnatin rikon kwarya yace sabbin shugabannin sojin sun bayyana aniyar su ta gudanar da zabe a watan Fabarairu mai zuwa da kuma mika mulki.

Kungiyar ECOWAS da AU duk sun dakatar da Mali sakamakon juyin mulkin da sojojin kasar suka yi sau biyu a cikin watanni 9, yayin da Faransa ta dakatar da aikin hadin gwuiwa wajen yaki da yan ta’adda da suke yi da sojojin Mali a yankin Sahel.

Goita ya karbi rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban kasar mulkin soji ranar litinin domin jagorancin gwamnatin rikon kwaryar da zata shirya zabe, kuma tuni ya nada Choguel Maiga a matsayin sabon Firaminista.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.