Burkina Faso - Ta'addanci

'Yan ta'adda sun tagayyara dubban mata da kananan yara a Burkina Faso

Wata mata a garin Gorom-Gorom dake arewacin Burkina Faso dake iyaka da kasar Nijar.
Wata mata a garin Gorom-Gorom dake arewacin Burkina Faso dake iyaka da kasar Nijar. © Photo by Issouf SANOGO / AFP

Hukumomin Burkina Faso sun ce mutane sama da 7,000 sun gudu daga wasu yankunan kasar sakamakon tashe tashen hankula da suka addabi kasar wanda ya haifar da zubda jini da kuma rasa rayuka na tsawon shekaru 6.

Talla

Firaministan Burkina Faso Christophe Dabire ya bayyana haka tserewar wadannan mutane sama da 7,000 zuwa wasu yankunan domin samun mafaka bayan ya ziyarci yankin da Yan bindiga suka kashe mutane sama da 130 a makon jiya.

Dabire yace suna daukar matakan tallafawa wadannan yan gudun hijira domin shawo kan matsalolin da suke fuskanta ta hanyar samar musu da matsuguni da abinci.

Masu baiwa gwamnatin shawara sun shaidawa kamfanin dillancin labaran AFP cewar adadin mutanen da suka gudu daga Solhan zuwa Sebba ya kai 7,600.

Kakakin Hukumar kula da yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya Babar Baloch ya ce mutane sama da 3,300 suka gudu, cikin su harda yara 2,000 da mata sama da 500 bayan Yan bindiga sun farma Solhan ranar asabar.

Akalla mutane 138 da suka hada da mata da maza da yara kanana Yan bindigar suna kashe, yayin da wasu kusan 40 suka samu raunuka.

Ministan sadarwar kasar Ousseini Tamboura yace yanzu haka kauyen Solhan ya zaam kango sakamakon tserewar da mazauna garin suka yi bayan harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.