WHO - Afrika

Kaso 90 na kasashen Afrika za su gaza kan shirin raba rigakafin Korona - WHO

Allurar rigakafin cutar Korona da kamfanin Johnson and Johnson ya samar.
Allurar rigakafin cutar Korona da kamfanin Johnson and Johnson ya samar. © Photo by Michael Ciaglo / GETTY IMAGES NORTH AMERICA / AFP

Hukumar lafiya ta duniya ta ce akwai yiwuwar kusan kashi 90 a kasashen Afrika za su gaza kan wa’adin yiwa al’ummominsu allurar rigakafin cutar Korona kafin watan Satumba, muddin basu gaggauta karbar sunkin alluran fiye da miliyan 200 ba.

Talla

A wani jawabi ta kafar intanet, daraktar sashin Afrika na hukumar lafiyar ta duniya Matshidiso Moeti, ta ce kasashe 7 cikin 54 na nahiyar ne ake kyautata zaton za su kai gaci a game da shirin yiwa al’ummominsu alluran rigakafin kafin cikar wa’adin da aka shata.

Akalla allurai miliyan 225 ne ake bukata cikin gaggawa idan har ana so akasarin kasashen su kai labari, kamar yadda kwararru suka tabbatar.

Kididdiga dai ta nuna kasa da kashi daya na alluran rigakafin Covid-19 sama da biliyan daya da miliyan 100 da aka rarraba a fadin duniya, nahiyar Afrika ta karba, a cewar hukumar lafiyar ta duniya.

Hakan yasa hukumar lafiyar ta bukaci kasashe masu hannu da shuni su taimaka wa kasashen da ba su da galihu domin samun daidaito wajen rabon alluran.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.