Burkina Faso - Ta'addanci

An gudanar da zanga-zanga kan rashin tsaro a Burkina Faso

Manifestation, devant le tribunal de Ouagadougou, au Burkina Faso, le 22 juin 2019, pour demander "la vérité et la justice" pour les victimes de l'attaque de Yirgou, au nord du Burkina Faso, qui a fait 49 mort le 1er janvier 2019.
Manifestation, devant le tribunal de Ouagadougou, au Burkina Faso, le 22 juin 2019, pour demander "la vérité et la justice" pour les victimes de l'attaque de Yirgou, au nord du Burkina Faso, qui a fait 49 mort le 1er janvier 2019. © AFP - OLYMPIA DE MAISMONT

Dubban mutane suka gudanar da zanga-zanga a Dori, dake arewacin Burkina Faso, don yin Allah wadai da halin rashin tsaro da kasar ke fuskata bayan kisan akalla mutane 132 a ƙauyen Solhan, wanda suke zarhin mahukunta da sakaci.

Talla

Masu zanga-zangar, wadanda suka taru a Dori, babban birnin yankin Sahel, suna rera wakon neman zaman lafiya a Sahel da Burkina Faso baki daya.

A ranakun 4 zuwa 5 na watan Yuni, mahara suka kashe aƙalla mutane 132, a kauyen Solhan dake kusa da kan iyakar kasar da Mali da Nijar, a cewar gwamnati, yayin da majiyoyin yankin sukace adadin wadanda aka kashe ya kai 160.

Hari mafi muni

Wannan harin shi ne mafi muni tun bayan fara rikicin dake da nasaba da mahara masu ikirarin jihadin a Burkina Faso shekaru shida da suka gabata, wanda ya yi sanadiyar mutuwar sama da mutane 1,400 tare da tilastawa miliyoyin mutane barin gidajensu.

Masu zanga-zangar sun je ofisoshin gwamnan, inda suka mika wata takarda da ke yin kira ga jerin matakan gaggawa na kare lafiyar mazauna da hanyoyi, in ji Yaya Dicko, daya daga cikin wadanda suka shirya taron.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.