Afirka - Coronavirus

Adadin wadanda suka harbu da korona a Afirka ya zarta miliyan 5

Wani dake karbar allurar rigakafin korona a Kigali na klkasar Rwanda ranar 18 ga watan Maris 2021
Wani dake karbar allurar rigakafin korona a Kigali na klkasar Rwanda ranar 18 ga watan Maris 2021 © REUTERS/Jean Bizimana

Fiye da mutane miliyan 5 ne a nahiyar Afirka suka kamu da cutar Covid-19 tun bayan bullarta a watan Disambar 2019 a kasar China.

Talla

Afirka ce Nahiyar da cutar bata yi mata illa ba sosai, ta yawan adadin masu kamawu da ita da ma wadanda ta kashe, bayan ga Oceania.

Alkaluman hukumomin lafiyar kasashe da kamfanin dillancin labarai na AFP ya tattara sun nuna cewa, mutane miliyan 5,008,656 suka harbu da cutar cikin kasashe da yankunan Afirka 54, kusan mutane 109,800 sun harbu ne cikin kwanaki bakwai da suka gabata, yayin da ta kashe sama da mutane dubu 134.

Bullar korona karo na uku

Yanzu haka wasu kasahen Nahiyar na fusknatar barazar barkewar cutar a karo na uku, inda ake kallon kasashen Masar da Afirka ta Kudu a matsayin kasashen da ke fama da bullar cutar a karo na uku, sai kuma Tunusia da Uganda da kuma Zambia da cutar ke kara tsanata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.