Cote d'Ivoire - Ta'addanci

Harin ta'addanci ya hallaka jami'an tsaron Cote d'Ivoire 3

Jami'an tsaron Ivory Coast dake sintiri a  Abidjan,ranar 4 ga watan Nuwambar 2020
Jami'an tsaron Ivory Coast dake sintiri a Abidjan,ranar 4 ga watan Nuwambar 2020 REUTERS/Luc Gnago

Akalla sojojin Ivory Coast biyu da wani dan sanda guda suka mutu jiya  Asabar lokacin da motarsu ta taka nakiya da aka binne a kan hanya a arewa maso gabashin kasar.

Talla

Majiyar tsaron kasar ta ce "fashewar ta kuma jikkata mutane uku ." Kuma hakan na zuwa mako guda bayan wani hari da wasu da ake zargin masu ikirarin jihadi ne suka kashe wani sojan Ivory Coast a garin Tougbo 'yan kilomita kadan daga kan iyaka da Burkina Faso.

Cibiyar horas da yaki da ta'addanci

Wannan harin na zuwa ne kwanaki biyu kacal bayan da Ivory Coast da Faransa suka kaddamar da wata makarantar horon yaki da ta’addanci a kusa da Abidjan da nufin bunkasa karfin yankin Sahel na dakile barazanar jihadi da ke yaduwa.

Masana harkar tsaro sun yi gargadin cewa kazamin yakin jihadi na yankin na iya bazuwa kudu zuwa kasashen da ke gabar tekun Guinea.

Karuwar hare-hare

Wannan shi ne karo na hudu da aka kai hari a kasar Cote d’ivore dake yankin yammacin Afirka cikin sama da watanni biyu.

Rikicin na baya-bayan nan ya fara ne tun a watan Maris, lokacin da wasu da ake zargin masu kishin Islama ne suka kashe wasu jami'an tsaron Ivory Coast uku a wani tagwayen samame da suka kai a kan sansanin sojoji a kusa da kan iyaka da Burkina.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI