Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya

Kwamitin tsaron MDD ya dakile shirin kai karin sojojin Rasha Afrika ta Tsakiya

Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a kauyen Yade, dake Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.
Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a kauyen Yade, dake Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya. © REUTERS

Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya dakile shirin kasar Rasha na aikewa da karin sojojin haya karkashin kamfanin Wagner zuwa Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.

Talla

Kwamitin tsaron ya ce ya dauki matakin ne sakamakon tuhumar da ake yiwa sojojin hayar na Rasha da aikata laifukan yaki da kuma take hakkin bil adama yayin kokarin murkushe ‘yan tawaye a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiyan, ciki har da harin da sojojin na Rasha suka kai kan iyakar kasar da Chadi, inda suka kashe dakarun Chadin 6 a ranar 30 ga watan Matun da ya gabata.

A wani labarin kuma, rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majlisar Dinkin Duniya MINUSCA, ta zargi sojojin hayar Rasha da hana dakarunta gudanar da ayyukansu na share nakiyoyin da ‘yan tawaye suka dasa a wasu sassan arewa maso yammacin kasar Afrika ta Tsakiyan.

Yayin karin bayani kan halin da ake ciki, kakakin rundunar wanzar da zaman lafiyar ta MINUSCA laftanar kanar AbdoulAziz Fall, ya dora alhakin matsalolin rashin hadin gwiwar da ake samu tsakaninsu da sojojin Afrika ta Tsakiya kan makarkashiyar sojojin hayar na Rasha ke shiryawa, wadanda ke kare kansu kan neman jinkirta aikin share nakiyoyin da hujjar kaddamar da farmaki kan mayakan ‘yan tawaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI