Tunisia

Zanga-zanga kan cin zalin 'yan sanda ta koma tarzoma a Tunisia

Masu zanga-zanga a yankin Sidi. Hassine dake wajen birnin Tunis a Tunisia.
Masu zanga-zanga a yankin Sidi. Hassine dake wajen birnin Tunis a Tunisia. © AFP

Arrangama ta barke tsakanin jami’an tsaro da gungun matasa a Tunis babban birnin kasar Tunisia a yayin da daruruwan matasan ke zanga-zangar nuna bacin rai kan cin zalin da ‘yan sanda ke a a Sidi Hassine dake birnin na Tunis.

Talla

Zanga-zangar ta barke ne dalilin mutuwar da wani ma’aikaci yayin da yake tsare a hannun ‘yan sanda a yankin na Sidi Hassine dake wajen birnin na Tunis.

Masu zanga-zangar sun yi  ta amfani da sanduna da kwalabe wajen kokarin yiwa jami’an tsaron dake kokarin tarwatsa su rotse, yayin da su kuma ‘yan sandan suka maida raddi ta karfi, abinda ya kai ga kame wasu daga cikin matasan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.