Somalia-Ta'addanci

Harim bom ya hallaka matasan da ake shirin dauka aikin Soja a Somalia

Motar da ke dauke da wadanda suka jikkata a farmakin na birnin Mogadishu.
Motar da ke dauke da wadanda suka jikkata a farmakin na birnin Mogadishu. REUTERS - FEISAL OMAR

Wani dan kunar bakin wake a kasar Somalia ya tayar da bam a inda ake aikin tantance matasan da za a dauka a matsayin sabbin sojoji da ke Mogadishu babban birnin kasar inda ya kashe mutum 15 daga cikinsu, yayin da wasu sama da 20 suka samu raunuka daban daban.

Talla

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ce wannan shi ne hari mafi muni da aka taba gani a cikin watanni 18 da suka gabata.

Mohammed Adan, wani shaidar gani da ido ya ce ya kidaya gawarwakin muatne 15 da kan sa, bayan afkuwar lamarin, yayin da jami’an aikin jinkai ke ta kai dauki.

Somalia na fama da hare-haren kungiyoyi masu ikirarin jihadi musamman al-Shebab wadda galibi kan kaddamar da farmakinta kan jami'an gwamnati wanda kan shafi tarin fararen hula tare da haddasa asarar dimbin rayuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI