Tafkin Chadi

Mutane miliyan biyar na fama da yunwa a Tafkin Chadi-MDD

Wata mata tare da yaranta a kauyen Tamou dake wajen birnin Yamai a Jamhuriyar Nijar.
Wata mata tare da yaranta a kauyen Tamou dake wajen birnin Yamai a Jamhuriyar Nijar. ASSOCIATED PRESS - TAGAZA DJIBO

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, mutane miliyan biyar da dubu 100 na fama da  yunwa a yankin Tafkin Chadi, sannan akwai yara sama da dubu 400 da ke fama da karancin abinci mai gina jiki a yankin. Wannan kuwa ba ya rasa nasaba da ayyukan masu da’awar jihadi.

Talla

Rahoton na Majalisar Dinkin Duniya ya ci gaba da cewa, a karon farko kenan tun bayan shekaru hudu da aka taba samun adadin mutane sama da miliyan biyar da suka fada cikin irin wannan ukuba.

Majalisar ta ce, sama da mutane miliyan goma ne ke bukatar agaji kuma sun fi yawa a arewacin Kamaru da yankin Diffa da ke kudu maso gabashin Nijar, sai kuma jihohin Adamawa da Borno da Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Dukkanin wadannan bangarorin sun fuskanci munanan hare-hare tun daga shekarar 2009 daga mayakan Boko Haram da kuma mayakan da ke da’awar jihadi a Yammacin Afrika wato ISWAP.

Tsawon shekaru 12 da aka dauka ana tashe-tashen hankula, ya haifar da manyan matsaloli ga mutanen yankin na Tafkin Chadi, wanda kungiyoyin bayar da agaji suka jima suna kiraye-kirayen shawo kan matsalolin da suka jefa mutane cikin bala’i.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce rikicin na yankin Tafkin Chadi ya tilasta wa sama da mutane miliyan biyu barin matsugunansu, baya ga kashe kusan dubu 36, kuma yanzu haka ‘yan Najeriya dubu 300 ne ke zaman gudun hijira a yankin Diffa da ke Jamhuriyar Nijar, wadanda suka tsere daga gidajensu tun a sahekarar 2015.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI