MOZAMBIQUE-KARUWANCI

Jami'an gidan yari na tilastawa mata karuwanci - Rahoto

Shugaban Mozambique Filipe Nyusi
Shugaban Mozambique Filipe Nyusi AFP/File

Wani bincike a kasar Mozambique da wata kungiyar yaki da cin hanci da rashawa ta gudanar ya bayyana cewar jami’an kula da gidan yarin kasar na tilastawa mata ‘yan gidan kaso aikin karuwanci da kuma azabtar da duk wadda taki yarda ayi lalata da ita.

Talla

Rahotan na Cibiyar Inganta Rayuwar Jama’a da aka wallafa yace ma’aikatan dake aiki a gidan yarin mata na Ndlavela a birnin Maputo na gabatar da mazan dake lalata da matan akan kudin da ya kai Dala 50 zuwa Dala 250 yayin da suke zuba kudin a cikin aljihun su.

Cibiyar da ta gudanar da binciken tace akan fitar da matan dake gidan yarin akalla sau 3 zuwa 4 kowanne mako zuwa gidajen baki domin amfani da su musamman ga manyan mutanen dake cikin al’umma.

Daraktan Cibiyar Edson Cortez ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar an kwashe sama da shekaru 10 ana tilastawa irin wadannan mata aikin karuwancin ba tare da hukumomi sun dauki matakin dakile shi ba.

Cortez yace jami’an sa da suka gudanar da binciken na watanni 6 sun badda kama kamar masu sha’awar matan inda suka yi amfani da na’urorin daukar hoto domin nadar abinda ke faruwa a asirce.

Sakamakon wannan rahoto yau ministan shari’ar kasar Helena Kida ta ziyarci gidan yarin inda ta bukaci binciken gaggawa kan lamarin nan da makwanni 2 masu zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI