Cote d’Ivoire - Gbagbo

Laurent Gbagbo ya koma Ivory Coast bayan shekaru 10 da kame shi

Tsohon shugaban kasar Cote d'Ivoire Laurent Gbagbo.
Tsohon shugaban kasar Cote d'Ivoire Laurent Gbagbo. Peter Dejong ANP/AFP/Archivos

Tsohon shugaban kasar Ivory Coast, Laurent Gbagbo, ya  koma gida yau alhamis bayan shafe kusan shekaru 10,  ya na fuskantar tuhuma daga kotun hukunta manyan laifuka ta Duniya ICC, sakamakon rawar da ya taka a haddasa rikicin da ya hallaka tarin ‘yan kasar a 2011.

Talla

Gbagbo mai shekaru 76 da yammacin yau ne jirginsa ya sauka a filin jirgin saman birnin Abidjan daga Brussels inda ya hadu da kasaitacciyar tarba musamman daga magoya bayansa, wadanda jami’an tsaro suka yi amfani da hayaki mai sanya hawaye don tarwatsa su bayan da suka yi dafifi a gab da filin jirgin.

Tsohon shugaban na Ivory Coast Laurent Gbagbo wanda ya mulki kasar daga shekarar 2000 zuwa 2011, rikici ya biyo bayan shan kayensa a zabe ne bayanda ya ki amincewa da faduwa.

Alkaluma na nuna yadda rikicin bayan zaben ya haddasa asarar rayukan mutane fiye da dubu 3 wanda ya sanya kame Gbagbo tare da gurfanar da shi a gaban kotun ta ICC.

Tun bayan wanke shi daga kotun ICC, Gbagbo ya samu mafaka a birnin Brussels na Belgium gabanin komawa kasar tasa ta Ivory Coast a yau alhamis.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.