Cote d’Ivoire - Gbagbo

Shirye-shiryen tarbar Gbagbo ya kankama a Abidjan

Tsohon shugaban kasar Cote d'Ivore Laurent Gbagbo, ranar 29 ga watan Oktobar 2010 aka dauki hoton.
Tsohon shugaban kasar Cote d'Ivore Laurent Gbagbo, ranar 29 ga watan Oktobar 2010 aka dauki hoton. ASSOCIATED PRESS - Rebecca Blackwell

Tsohon shugaban kasar Ivory Coast, Laurent Gbagbo, zai koma ranar Alhamis bayan shafe kusan shekaru 10 da barin kasar da yaga daukaka da kuma wulakanci cikin tsawon lokacin da ya kwashe yana mata aiki.

Talla

Gbagbo mai shekaru 76 na shirin komawa kasar da ya yi mulka tsakanin shekarar 2000 zuwa 2011, bayan da Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya (ICC) da ke Hague ta tabbatar da wanke shi daga laifukan cin zarafin bil'adama.

Kin amincewa da shan kaye

Tuhume-tuhumen sun sama asali ne daga rikicin da aka kwashe watanni biyar ana yi sanadiyyar kin amincewa da Gbagbo ya yi da shan kaye a zaben shekarar 2010 bayan da abokin karawarsa Alassane Ouattara ya samu nasara, nasarar da Majalisar Dinkin Duniya ta amince.

Fiye da mutane 3,000 aka kashe kafin a cafke Gbagbo a cikin cibiyar tattalin arziki kasar Abidjan a ranar 11 ga watan Afrilun shekarar 2011, sannan a tisa keyarsa zuwa kotun ICC.

Faransa na da hannu

Gbagbo ya zargi Faransa da ta yi wa Ivory Coast mulkin mallaka, da hannu a wani makirci da ya kai ga sojojin Ouattara suka kame shi, a inda ya buya a karkashin kasa.

Farin jinin "Zakin Afirka"

Ga dukkanin alamu rashin kasancewarsa a kasar na dogon lokaci bai rage masa farin jini, domin kuwa rahotanni sun ce dubbun magoya bayan sa na shirye-shiryensa tarbarsa Abidjan.

A garinsa na Gagnoa da ke tsakiyar yammacin Ivory Coast, shirye-shirye su kankama don tarbar mutumin da suke gani gwarzo da lakabi da "Zakin Afirka".

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI