Mali - Faransa - Ta'addanci

Rundunar Barkhane ta cafke wani jigon 'yan ta'addan Mali

Rundunar sojin Faransa ta Barkhane dake yaki da ta'addanci a Mali.
Rundunar sojin Faransa ta Barkhane dake yaki da ta'addanci a Mali. Daphné BENOIT AFP/File

Rundunar sojin Faransa ta Barkhane ta sanar da cafke wani da aka bayyana cewa jigo ne a kungiyar masu da’awar jihadi a yankin Sahara da ake kira (EIGS).

Talla

Sanarwa da ma’aikatar tsaron Faransa ta fitar a jiya laraba, na cewa an cafke Dadi Ould Chouaib da ake kira Abou Dardar, wanda aka jima ana nema bayan tabbatar da cewa shi ne ya jagoranci kire wa wasu mutane biyu gabobi ranar 2 ga watan mayun da ya gabata a kasuwar Tin Hama da ke arewacin kasar ta Mali.

Bayanai sun ce an cafke Abou Dardar ne ba tare da ya nuna wata tirjiya ba, duk da cewa a lokacin yana dauke da karamar bindiga sannan sanye da riga mai sulke tare da wasu wayoyin sadarwa tare da shi.

Sanarwar ta ce an cafke shi ne a ranar 11 ga wannan wata na yuni a kusa da iyakokin kasashen Nijar, Mali da kuma Burkina Faso, yankin da ake kallo a matsayin babbar matattarar masu da’awar jihadi.

Shi dai Abou Dardar, ya kasance jigo a tsohuwar kungiyar masu jihadi da ake kira Mujoa, kuma an taba kama shi a shekara ta 2014 tare da mika shi a hannun mahukuntan Mali, wadanda suka sallame shi tare da wasu mutane 200 karkashin yarjejeniyar musayar fursunoni kafin sakin wata bafaransa mai suna Sophie Pétronin a shekara ta 2020.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.