Zambia

Tsohon shugaban Zambia Kenneth Kaunda ya mutu yana da shekaru 97

Tsohon shugaban kasar Zambia Kenneth  Kaunda.
Tsohon shugaban kasar Zambia Kenneth Kaunda. STEFAN ZAKLIN GETTY IMAGES NORTH AMERICA/AFP

Tsohon shugaban kasar Zambia Kenneth Kaunda ya mutu yau ya na da shekaru 97 bayan fama da cutar toshewar hanyoyin lumfashi da ta kai shi ga kwanciya a asibiti na ‘yan kwanaki.

Talla

Kaunda shugaba mafi dadewa a kujerar mulkin kasar Zambia, ya shafe shekaru 27 yana jan ragamar kasar tun bayan samun ‘yancin kai daga birtaniya a 1964 gabanin tsarin demokradiyya ya yi awon gaba da kujerarsa.

Kaunda wanda ya yi gwagwarmayar kalubalantar turawan mulkin mallaka ana kallonsa a matsayin jajirtaccen jagora ba kadai ga kasar sa ta Zambia ba harma da nahiyar Afrika baki daya.

A litinin din da ta gabata ne aka garzaya da Kaunda asibiti bayan tsanantar cutar ta sa yayinda rai ya halinsa a yau litinin.

Kenneth Kaunda shi ne shugaban farko da Nelson Mandela ya ziyarta a shekarar 1990 bayan fitowa daga kurkuku, yayinda ya ke matsayin na karshe a jerin jagororin Afrika da suka yi gwagwarmayar neman 'yanci daga turawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI