Burkina Faso

Burkina Faso na taron masu ruwa da tsaki tare da 'yan adawa kan ta'addanci

Dakarun Faransa yayin sintiri a yankin arewacin kasar Burkina Faso.
Dakarun Faransa yayin sintiri a yankin arewacin kasar Burkina Faso. AFP via Getty Images - MICHELE CATTANI

Burkina Faso ta kaddamar da wani taron kwanaki biyu tsakanin bangarorin gwamnati da jam’iyyun adawa domin neman mafita daga matsalar karuwar hare-haren ta’addanci a kasar.

Talla

Wannan taro  da shugaban kasar Roch Marc Christian Kabore ya gabatar, na zuwa ne a daidai lokacin da hare-haren mayaka masu ikirarin jihadi ke yawaita a kasashen yankin Sahel.

A ranar 5 ga Yuni, aƙalla mutane 132 aka kashe a hare-haren da aka kai cikin dare a yankin Solhan, kusa da kan iyaka da Mali da Nijar.

Adadin rayukan da suka salwanta yayin farmakin na yankin Solhan shi ne mafi muni da kasar Burkina Faso ta gani tun bayan soma fuskantar rikicin ta’addanci shekaru. 6 da suka gabata.

A farkon watan Yuni, hukumomin Burkina Faso suka ce mutane sama da dubu 7 sun gudu daga wasu yankunan kasar sakamakon tashe tashen hankula da suka addabi kasar wanda ya haifar da zubda jini da kuma rasa rayuka na tsawon shekaru 6.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.