Mali - Siyasa

Bukatar yan siyasa bangaren adawa ga gwamnati kasar Mali

Choguel Kokalla Maïga Firaministan wucin gadi tareda wasu daga cikin yan siyasar kasar Mali
Choguel Kokalla Maïga Firaministan wucin gadi tareda wasu daga cikin yan siyasar kasar Mali AFP - MICHELE CATTANI

A Mali ,wasu daga cikin shugabanin jam’iyoyin siyasa bangaren adawa na ci gaba da bayana damuwa ganin salon tafiya da majalisar soji ta rikon kwariya ke gudanar da mulkin wannan kasa.

Talla

Jam’iyyar Parena a karkashin Shugabancin Tiebile Drame na fargabar ganin Firaministan kasar Choguel Kokalla Maïga ya hada baki da sojoji da nufin tsawaita lokacin da ya dace su mika ragamar mulki ga farraren fula.

Choguel Kokalla Maïga  Firaministan rikon kwariyar kasar Mali
Choguel Kokalla Maïga Firaministan rikon kwariyar kasar Mali AFP/Seyllou

A hukumance Sojoji dake rike da mulki a yanzu haka sun dau alkawalin mika mulki bayan watani 18 na rikon kwariya duk da cewa an fuskanci wani juyin mulki na biyu a watan Mayu,shugaban majalisar sojin kasar Assimi Goita ya ce babu tattanma zai mika mulki,alkawarin da wasu yan siyasa da kungiyoyi dake fafutukar kare hakokin bil Adama a kasar ke ta nuna shaku a kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI