Guinea - Ebola

Hukumar Lafiya ta sanar da kawo karshen cutar Ebola a Guinee

Jami'an kiwon lafiya na yiwa yan kasar Guinee allurar Ebola
Jami'an kiwon lafiya na yiwa yan kasar Guinee allurar Ebola CAROL VALADE AFP

Hukumar lafiya ta Duniya a hukumance a yau asabar ta tabbatar da kawo karshen cutar Ebola a kasar yan watanni bayan sake bulluwar ta a watan janairun shekarar bana.

Talla

Idan aka yi tuni karo na farko kenan da cutar ta bulla a Guinea cikin shekaru 5, bayan barnar da ta tafka a kasar da makwaftanta na Liberia da Saliyo a tsakanin shekarun 2013 zuwa 2016, inda ta lakume rayukan mutane dubu 11 da 300 a tsakanin kasashen.

Wasu daga cikin akwatina dauke da allurar Ebola.
Wasu daga cikin akwatina dauke da allurar Ebola. © RFI / Carol Valade

Tun a wanccan lokacin ne kuma, kwararru suka samar da allurar rigakafin cutar ta Ebola, tare da tara sunkin maganin akalla dubu 500, domin shirin ko ta kwana idan annobar ta sake barkewa.

 

Daya daga cikin jami’an hukumar kiwon lafiya ta Duniya  mai suna Alfred  Ki Zerbo yayin wani biki a kauyen  Nzerekore dake kudu maso gabashin kasar, yankin da cutar ta sake bulluwa a baya a watan Janairun  shekarar  bana da babbar murya yake mai cewa cikin farin ciki yake mai bayyana kawo karshen  cutar Ebola a kasar ta Guinee ga baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI