ECOWAS

Rikicin Mali da kudin bai daya za su mamaye taron ECOWAS na tsakiyar shekara

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan dake jagorantar tawagar kungiyar ECOWAS masu shiga tsakanin rikicin siyasar kasar Mali.
Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan dake jagorantar tawagar kungiyar ECOWAS masu shiga tsakanin rikicin siyasar kasar Mali. AFP - NIPAH DENNIS

Yau Asabar shugabannin kasashen ECOWAS ke ganawa a Accra babban birnin kasar Ghana, a taron tsakiyar shekara da ke zama karo na 59.

Talla

Manyan batutuwan da da taron zai maida hankali kai sun hada da makomar shirin yiwa tsarin ayyukan kungiyar ta ECOWAS garambawul, makomar shirin soma amfani da takardar kudin bai daya tsakanin kasashen na yammacin Afrika, da kuma makomar siyasa da shugabancin kasar Mali da sojoji suka yi juyin mulki sau 2 cikin watanni 9.

Yayin taron na yau kuma tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan jakadan musamman wajen sasanta rikicin siyasar Mali, zai gabatar da jawabi kan rahoton da ya tattara kan ziyarar aikin da ya kai kasar ta Mali a baya bayan nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI