Uganda - Jamhuriyar Congo

Uganda ta sake killace yan kasar na makonni 6 sabili da cutar Covid 19

Shugaban kasar Uganda Yoweri Kaguta Museveni.
Shugaban kasar Uganda Yoweri Kaguta Museveni. via REUTERS - PRESIDENTIAL PRESS SERVICE

A jiya juma’a Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni ya sanar da sabin matakan da hukumomin kasar suka dau na sake killace kasar don hanna yaduwar cutar Covid 19.

Talla

Daga cikin matakan da Shugaban kasar ya sanar,an hana duk wani balaguro cikin kasar na tsawon makonni shida, tareda hana duk wasu harakoki da suka shafi sufuri, sai dai Shugaban ya bayyana cewa kan iyakokin kasar za su kasance a bude, wata hanyar baiwa yan yawon bude ido damar shiga kasar da kuma baiwa  yan kasuwa damar shigowa da kayakin masarufi.

Allurar rigakafin cutar Covid 19
Allurar rigakafin cutar Covid 19 CHANDAN KHANNA AFP/Archivos

Kasar ta Uganda na daga cikin kasashen da cutar  Covid 19 ke ci gaba da yiwa barazana duk da kokarin  hukumomin kasar na takaita yaduwar cutar a dan tsakanin nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI