Charles Ble Goude na fatan komawa Cote D'Ivoire
Wallafawa ranar:
Yayinda tsohon Shugaban kasar Laurent Gbagbo ya koma gida ranar 17 ga wannan watan da muke cikin sa ,kalo ya koma bangaren gwamnatin Alassane Ouattara na ganin ta gaggauta samarwa tsohon Ministan matasa makusancin tsohon Shugaban kasar, Charles Ble Goude wanda ya kasance a tsare tareda Gbagbo kusan shekaru 10,takardar Fasfo.
tsohon Ministan matasa Charles Ble Goude ya bayyana cewa kusan watanni uku kenan yake dakon wannan takarda daga hukumomin Abidjan, masu magana da yahun Charles Ble Goude sun bayyana cewa sun samu ganawa da Ministan dake da nauyin sassanta yan kasar,wanda ya kuma dau alkawali warware wannan matsalla da farko,kafin daga bisali a mayar da hankali dangane da batun dawwowar sa gida kamar dai yada tsohon Shugaban kasar Gbagbo yayi a baya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu