Gwamnatin Chadi ta musanta zagin kisan yan tawayen FACT

Wasu daga cikin magoya bayan jam'iyya mai mulkin kasar Chadi
Wasu daga cikin magoya bayan jam'iyya mai mulkin kasar Chadi AFP - MARCO LONGARI

Gwamantin rikon kwariyar kasar Chadi ta mayar da martani biyo bayan zargin ta tareda shigar da kara zuwa kotun hukunta manyan laifuka da wasu kungiyoyi suka yi na cewa kamata a gudanar da bincike dangane da kisan mayakan kungiyar yan tawayen FACT da wasu farraren hula da ake zargin dakarun kasar Chadi da aikatawa bayan mutuwar tsohon Shugaban kasar Idriss Deby.

Talla

 

Ministan  sadarwa na kasar ta Chadi Aberaman Koulamallah wanda ke da mukamin mai magana da yahun gwamnatin kasar ya bayyana cewa ana kokarin shafawa  hukumomin kasar kashin kaji ne, jami’in ya bayyana cewa kungiyoyi da dama ne suka ziyarci  fursunoni dake tsare yanzu haka, suna cikin koshin lafiya, banda haka, batun kisan farraren hula ba gaskiya bane.

 

Max Loalngar (au centre), leader de la coordination des actions citoyennes de Wakit Tamma, Barka Michel et Citak Yombatinan, en conférence de presse le 8 juin, à Ndjamena.
Max Loalngar (au centre), leader de la coordination des actions citoyennes de Wakit Tamma, Barka Michel et Citak Yombatinan, en conférence de presse le 8 juin, à Ndjamena. AFP - DJIMET WICHE

Gwamnatin rikon kwariyar Chadi na ci gaba da musanta wannan zargi da kungiyoyi ke yi mata,ta kuma bayyana cewa ta na a shirye don ganawa da duk masu bukata daga cikin dama wajen kasar ta Chadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI