WHO - Afrika

Hayakin sigari na halaka miliyan 146 duk shekara a Afrika

Sigari na sanadin mutuwar miliyoyin mutane duk shekara a nahiyar Afrika.
Sigari na sanadin mutuwar miliyoyin mutane duk shekara a nahiyar Afrika. © AFP

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce kimanin mutane miliyan 146 ke mutuwa duk shekara a Afrika a dalilin fama da cutuka masu nasaba da shan taba sigari kai tsaye ko kuma ta hanyar shakar hayakin da mai shan tabar ke fitarwa.

Talla

Yayin ganawa da manema Labarai ta kafar bidiyo a makon da ya kare, babbar darakatar hukumar WHO a nahiyar Afrika dakta Matshidiso Moeti ta jaddada gargadin cewar busa taba sigari na kassara kusan dukkanin sassa masu muhimmanci a jikin dan adam.

Dakta Moeti ta kuma ce binciken kwararru a baya bayan nan, ya gano cewar fiye da mutane miliyan 1 da dubu 2 ke rasa rayukansu, sakamakon cutuka masu alaka da shakar hayakin da mai shan taba sigari ke fitarwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.