Guinea - Ebola

WHO ta yi shelar kawo karshen annobar Ebola a Guinea

Wani jami'in lafiya dake aikin dakile yaduwar annobar Ebola a Guinea.
Wani jami'in lafiya dake aikin dakile yaduwar annobar Ebola a Guinea. © Carol Valade/RFI

Hukumar Lafiya ta Duniya da kuma ma’aikatar lafiyar Guniea,  sun yi shelar kawo karshen annobar Ebola da ta sake barkewa a kasar cikin watan Fabarairu.

Talla

Bikin samun nasarar kawar da cutar ya gudana ne a yankin Nzerekore dake kudu maso gabashin kasar ta Guinea, inda annobar ta sake bayyana a farkon wannan shekara.

Da fari kwararru sun bayyana faragaba kan yiwuwar sake yaduwar annobar zuwa wasu kasashen yammacin Afrika, amma daga bisani aka samu nasarar dakile ta, matakain da ya takaita hasarar rayukan da aka samu dalilin cutar zuwa 12 daga cikin 16 da suka kamu.

A shekarun 2014 zuwa 2016 dai mutane akalla dubu 11 da 300 annobar Ebola ta kashe a wasu kasashen yammacin Afrika, musamman a Saliyo, Guinea, da kuma Liberia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.