Yan gudun hijira na rayuwa cikin barazana a Duniya (MDD)
Wallafawa ranar:
Yau ce ranar da Majalisar dinkin Duniya ta ware a matsayi ranar yan gudun hijira a Duniya, ranar dake zuwa a daidai lokacin da dubban yan gudun hijra ke fuskantar tarin matsalloli, sabili da yaki da dama suka baro gidajen su.
A Jamhuriyar Tsakiyar Afrika,kusan yan gudun hijira 8.500 aka kora da wani sanssani dake birni na hudu a kasar,a cewar kungiyar lokitoci ta kasa da kasa Medecin Sans Frontiere.
Da jimawa gwamnatin kasar na kalon wannan wuri a matsayin wata maboya ga yan tawaye dake fakewa a wannan sanssani da suke anfani da shi domin kai dakarun gwamnatin kasar hari.
Gwamnatin kasar ta yaba da jan kokarin dakarun Rasha dake ci gaba da kawo ta su gundunmuwa don sake kwato wasu yankuna dake hannun yan tawaye yanzu haka..
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu