Habasha-Zabe

Habasha na zabe cikin yanayin yunwa da yaki

Masu kada kuri'u a Habasha
Masu kada kuri'u a Habasha REUTERS - BAZ RATNER

Al’ummar Habasha na kada kuri’a a wannan Litinin a zaben da aka jinkirta wanda ke zuwa a daidai lokacin da kasar ke fama da yaki da yunwa a yankin Tigray, yayin da ake diga ayar tambaya kan sahihancin zaben.

Talla

A karon farko tun bayan darewarsa kan karagar mulki a 2018, Firaminista Abiy Ahmed mai shekaru 44 na   fuskantar Habashawa masu kada kuri’a a zaben kasar wadda ita ce ta biyu mafi yawan al’umma a nahiyar Afrika.

Abiy wanda ya  lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel ya yi afuwa ga fursunonin siyasa tare da tarbar masu laifin da suka dawo kasar bayan sun tsare daga cikinta, yayin da ya kawo karshen yakin cacar-baka da makwabciyar kasar, wato Eritrea.

Firaministan ya yi wa al’umar Habasha alkawarin gudanar da zabe mafi zafi a tarihin kasar kuma wanda zai kasance sahihi da zai banbanta da zabukan da aka gudanar a can baya.

A yayin kada kuri’arsa a mahaifarsa da ke garin Beshasha a tsakiyar Habasha, Firaminista Abiy ya ce, daukacin masu fafatawa a wannan zabe sun cancaci girmamawa duk kuwa da yadda sakamakon zaben zai kasance.

Mutane da dama sun shafe  tsawon sa’o’i a kan dogayen layuka don jefa kuri’unsu a zaben wanda jam’iyyu da yawa ke takara a cikinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.