Mali-ECOWAS

Dakatarwar da ECOWAS ta wa Mali na nan daram

Kanar Assimi Goita jagoran juyin mulkin Mali.
Kanar Assimi Goita jagoran juyin mulkin Mali. AP

Kasashen yammacin Afrika dake karkashin kungiyar ECOWAS sun ce za su cigaba da bibiyar yadda lamurra ke tafiya a kasar Mali, kafin su janye hukuncin dakatar da ita daga cikinsu da suka yi, sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi har sau biyu cikin watanni 9.

Talla

Juyin mulkin na Mali dai ya sanya Faransa dake da dakaru fiye ad dubu 5 a kasar, dakatar da aikin hadin gwiwar da suke yi ta fuskar soji wajen yaki da ta’addanci a sassan kasar da kuma yankin Sahel.

A makwannin baya jagoran sojojin da suka yi juyin mulki a kasar ta Mali Kanal Assimi Goita ya sanar da kafa sabuwar gwamnatin rikon kwarya da ta kunshi fararen hula ko da yake mafi akasarin muhimman mukaman sojoji ne suka ci gaba da rikewa.

Kanal Assimi Goita yayi alkawarin shirya zaben da zai maidawa fararen hula mulki a watan Fabarairun dake tafe kamar yadda aka cimma matsaya a ciki da wajen kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.