WHO-Afrika

WHO za ta kafa cibiyar sarrafa rigakafin Korona a Afrika

An bar al'ummar Afrika a baya wajen yi musu rigakafin cutar Korona
An bar al'ummar Afrika a baya wajen yi musu rigakafin cutar Korona AFP - BADRU KATUMBA

Hukumar Lafiya ta Duniya za ta kafa babbar cibiyar sarrafa allurar rigakafin kariya daga cutar Korona don wadatar da ita ga kasashen Afirka, cibiyar da za ta kasance a kasar Afirka ta Kudu.

Talla

Shugaban Hukumar Lafiyar ta WHO Tednos Adhanom Gebreyesus, ya ce ko baya ga sarrafa allura, wannan cibiya za ta samar da horo ga sauran kasashen nahiyar.

Gebreyesus ya ce, wannan gagarumin aiki ne da wasu kamfanoni masu kwarewa za su gudanar a matsayin hadin gwiwa.

Wannan kawance ne da zai hada kamfanoni da dama ciki har da African Biologics and Vaccines da zai taka rawa wajen ganin an sarrafa allurar da kuma samar da horo ga jami’an wani kamfanin da zai rika sarrafa allurar mai suna Bioback. Sai kuma wani kamfanin wanda zai ci gaba da bayar da horo kan yadda ake sarrafa allurar a cikin sauran kasashen Afirka. inji Gebreyesus.

Wannan albishir ne da ya yi matukar gamsar da mahukuntan kasar Afirka ta Kudu, inda shugaban kasar Cyril Ramaphosa ke cewa. "Saboda rashin daidaito wajen samar da wannan allura, hakan ya sa al’ummomin da ke rayuwa a kasashe masu karfin tattalin arziki suka fi samun kulawa fiye da mutanen da ke rayuwa a kasashen da ke fama da talauci."

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da ya kasance jigo a kokarin da ake yi na samar da wannan allura musamman ma a cikin kasashen Afirka, ya bayyana wannan sabon shiri a matsayin gagarumin ci gaba, yana mai cewa, "Wannan muhimmiyar rana ce ga nahiyar Afirka, inda kowace kasa za ta samu damar kirkira da kuma sarrafa wannan magani."

Yayin da wasu kasashe suka yi nasarar yi wa akasarin al’ummominsu allurar kariya daga wannan cuta, a Afirka kuwa duka-duka adadin wadanda suka samu allurar ba zai zarta 2% ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI