Kamaru - coronavirus

Kamaru ta karbi allurar rigakafin korona sama da miliyan 5 daga Amurka

Allurar rigakafin korona na Johnson & Johnson na kasar Amurka.
Allurar rigakafin korona na Johnson & Johnson na kasar Amurka. AP - Mary Altaffer

Gwamnatin Kamaru ta yi odar allurar rigakafin kariya daga cutar korana samfurin Johnson & Johnson har guda milyan 5 da dubu 300 daga kasar Amurka.

Talla

Gwamnatin Kamaru ta ce ta yi odar wadannan allurai ne domin tabbatar da cewa ta yi wa akalla 20% na al’ummar kasar rigakafin kariya daga wannan cuta kafin fara gasar neman kofin kwallon kafa na Afirka da za a yi a kasar daga watan janairu zuwa fabarairun shekara mai zuwa.

Yau kimanin watanni uku kenan da aka kaddamar da shirin allurar rigakafin kariya daga cutar ta Covid-19 ta hanyar amfani da maganin Sinopharm da kuma Astrazeneca, to sai dai adadin alluran da ake da su a halin yanzu ya yi kadan, saboda haka aka yi odar Johnson & Johnson a cewar gwamnatin.

Domin tabbatar da samun nasarar wannan rigakafi, a ranar 16 ga wannan wata ne ministan lafiyar kasar Manaouda Malachie ya sanar da cewa jami’an kiwon lafiya za su gudanar da wani gagarumin shirin rigakafi daga ranar 7 zuwa 11 ga watan yuli mai zuwa a duk fadin kasar.

Alkaluman ma’aikatar lafiyar Kamaru, na nuni da cewa kafin ranar 16 ga wannan watan Yuni, daga cikin mutane dubu 70 da 300 da aka yi wa wannan allura, duka duka dubu 16 da 200 suka karbi zagaye na biyu na allurar a kasar wadda aka samu asarar rayukan mutane dubu 1 da 310 sakamakon kamuwa da cutar ta korona.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.