Cote d'Ivoire

Kotun Cote d'Ivoire ta yankewa Guillaume Soro daurin rai-da-rai

Tsohon Franministan Ivory Coast Guillaume Soro, a Paris a a watan Satumbar shekarar 2020
Tsohon Franministan Ivory Coast Guillaume Soro, a Paris a a watan Satumbar shekarar 2020 STEPHANE DE SAKUTIN / AFP

Kotu a Cote d’Ivoire ta zartas da hukunci daurin rai-da rai ga tsohon Firaministan kasar, kuma tsohon madugun 'yan tawayen kasar Guillaume Soro dake gudun hijira, sakamakon laifin yunkurin wargaza kasa.

Talla

Baya ga Guillaume Soro, kotu ta kuma yanke hukuncin ga wasu daga cikin mukaraban sa da ake zargi da hada baki da tsohon Madugun 'yan tawayen kasar, wandada aka kuma yankewa hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari.

Sai kuma wasu daga cikin sojojin kasar 7 da kotun ta samu da laifin tada tarzoma, wadanda kuma ta yankewa hukuncin daurin watanni 17 ko wannensu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.