Rikicin kasar Libya

Manyan kasashen duniya na taron neman zaman lafiya a Libya

Masu dauke da makamai a kasar Libya
Masu dauke da makamai a kasar Libya Mahmud TURKIA AFP/File

Manyan kasashen duniya na taro a Berlin na kasar Jamus domin lalubu hanyoyin samar da dawwamammen zaman lafiya a kasar Libya, ta yadda zata tsaya da kafafunta wajen samun gudanar da zaben a ranar 24 ga watan Disamba.

Talla

Taron wanda Majalisar Dinkin Duniya ta dauki nauyi ya samu halartar Firayiministan gwamnatin rikon kwartar Libya Abdul Hamid Dbeibah da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken da kuma ministocin harkokin wajen Faransa da Turkiya da kuma Masar.

Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov bai halarci taron ba, amma Mataimakin sa Sergey Vershinin ya wakilce shi.

Franminstan rikon kwarayar Libya Abdel Hamid Dbeibah yayin ganawa da shugaban Faransa Emmanuel Macron a 'Elysée ranar 1 ga watan Yuni 2021.
Franminstan rikon kwarayar Libya Abdel Hamid Dbeibah yayin ganawa da shugaban Faransa Emmanuel Macron a 'Elysée ranar 1 ga watan Yuni 2021. AFP - GEOFFROY VAN DER HASSELT

Wannan dai shine taro karo na biyu dake gudana a Berlin a Kokarin manyan kasashen duniya na kawo karshen tashin hankalin da aka kwashe sama da shekaru goma ana gwabzawa a kasar Libya.

Bayan wanda aka gudanar a shakarar 2020, kafin annobar korona, wanda shugabannin kasashen Turkiya da Rasha da Faransa suka.

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinkin, ya bukaci janye sojojin kasashen waje dake cikin kasar dake fama da rikici a Arewacin Afirka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.