Cote d’Ivoire - Soro

Guillaume Soro ya yi watsi da hukuncin daurin rai da rai

Guillaume Soro tsohon Firaminista kuma tsohon jagoran 'yan tawaye na Ivory Coast.
Guillaume Soro tsohon Firaminista kuma tsohon jagoran 'yan tawaye na Ivory Coast. Stéphane de Sakutin AFP/Archivos

Tsohon Firaministan Ivory Coast kuma tsohon madugun ‘yan tawaye Guillaume Soro ya yi watsi da hukuncin daurin rai da rai da kotun kasar ta yanke masa jiya Laraba a birnin Abidjan.

Talla

Soro a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter ya ce ko kadan ba zai amince da hukuncin kotun ba wanda ya bayyana a mai cike da son kai da karya ka’idojin shari’a baya ga fifita hamayyar siyasa maimakon zartas da hukunci yadda doka ta tanada.

A cewar Soro mai shekaru 49 wanda ke matsayin tsohon na hannun daman shugaba Alassane Ouattara, ba komi ke tattare da hukuncin ba sai kokarin shafe babin siyasarsa a kasar, yayinda ya sha alwashin daukaka kara don samun adalci.

Hukuncin na Soro dai ya biyo bayan samunsa da laifin hada kai da wasu Soji baya ga fararen hula a kokarin juyin mulki ga shugaba Ouattara a bara, wanda ya kai ga zartas musu da hukuncin a jiya laraba.

Ko a bara Ivory Coast ta hana Soro damar tsayawa a takarar neman kujerar shugabancin kasa bayan zarginsa da badakalar kudi.

Baya ga Soro wasu mutu biyu sun fuskanci hukuncin kotun a zaman na yau, ciki har da Souleymane Kamagate da Affoussy Bamba wadanda za su shafe shekaru 20 20 a gidan yarin saboda taimakawa soro baya ga Wasu Soji 7 da kuma ‘yan uwan soro 2 da za su yi watanni 17 kowannensu a gidan yari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.