Habasha-Zabe

Kungiyar AU ta tabbatar da ingancin yadda zabe ya gudana a Habasha

Wasu layin kada kuri'a yayin zaben Habasha.
Wasu layin kada kuri'a yayin zaben Habasha. © BAZ RATNER/REUTERS

Tawagar kungiyar Tarayyar Afrika da ta sanya idanu kan zaben Habasha ta tabbatar da sahihancin yadda zaben ya gudana dai dai lokacin da ake ci gaba da aikin kidayar kur’u.

Talla

Tawagar ta kungiyar AU ta ce ta ganewa idonta yadda gwamnati ta gudanar da shirye-shiryen zaben dama yadda aka gudanar da shi ba tare da fuskantar kalubale ba a ilahirin sassan kasar.

Sau biyu Habasha na dage zaben wanda a farko aka tsara gudanar da shi cikin watan Agustan 2020 amma coronavirus ta hana daga baya kuma matsalolin tsaro suka kawo cikas bayan sanya ranar 5 ga watan nan don gudanar da shi.

A Litinin din da ta gabata ne, al’ummar Habashan suka kada kuri’a a zaben na yankuna da jihohi wanda ke matsayin irinsa na farko da Abiy Ahmed ke gani a matsayin shugaba.

Sai dai hukumar zaben Habashan tun gabanin ranar kada kuri’a ta sanar da dage zaben a wasu yankuna da ke fuskantar rikici da kuma karancin tsaro wanda aka tsare nasu zaben zai gudana a watan Satumba mai zuwa.

Zaben ya zowa Abiy Ahmed dai dai lokacin da ya ke fuskantar takun saka da manyan kasashen Duniya musamman kan rikicin yankin Tigray da ake zargin Sojinsa da farmakar fararen hula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.