Afrika - Tattalin Arziki

'Yan Afrika miliyan 30 sun talauce saboda Korona - AFDB

Wani yankin marasa karfi a kasar Afrika ta Kudu.
Wani yankin marasa karfi a kasar Afrika ta Kudu. © REUTERS/SIPHIWE SIBEKO

Shugaban bankin raya kasashen Afrika AFDB Dakta Akinwumi Adesina, ya ce tattalin arzikin nahiyar Afrika ya tafka hasarar fiye da dala biliyan 190 saboda tasirin annobar Korona.

Talla

Adesina ya bayyana wannan rahoton ne a lokacin da yake jagorantar taron hukumar gudanarwar bankin na AFDB na shekara shekara ta kafar bidiyo a wannan makon.

Shugaban bankin ya kara da cewar baya ga hasarar ta fiye da dala biliyan 190 ga tattalin arzikin kasashen na Afrika, barkewar annobar Koronar ta jefa mutane akalla miliyan 30 cikin kangin talauci, yayin da wasu miliyan 39 kari ke cikin hatsarin fadawa talaucin a karshen shekarar 2021.

Sai dai Adesina ya bayyana kwarin gwiwar shawo kan matsalar, la’akari da shirin da bankin Afrikan ya kaddamar na ware dala biliyan 3 domin taimakawa kasashen nahiyar wajen farfado da tattalin arzikinsu, ciki har da dala miliyan 28 da bankin ya warewa cibiyoyin dakile yaduwar cutuka na kasashen Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.