Mozambique-Ta'addanci

'Yan ta'adda sun zafafa farmaki kan garuruwan arewacin Mozambique

Yankin Palma da ke karkashin ikon kungiyoyi masu ikirarin jihadi a Mozambique.
Yankin Palma da ke karkashin ikon kungiyoyi masu ikirarin jihadi a Mozambique. © LUSA - João Relvas

Wasu rahotanni daga Mozambique sun bayyana yadda hare-haren kungiyoyi masu ikirarin jihadi ya rutsa da tarin fararen hula ciki har da Mata da kananan yara a yankin Cabo Delgado na arewacin kasar.

Talla

Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya ruwaito cewa yanzu haka gwamnatin Mozambique ta amince da girke tarin dakarun tsaro hadakar kasashen kudancin Afrikan don yaki da ta’addancin da ya addabi kasar.

Majiyar tsaron kasar ta tabbatar da wani farmakin mayakan ta’addancin a jiya laraba wanda ya kai ga artabu tsakanin mayakan masu ikirarin jihadi da Sojin kasar a garin Palma da ke arewaci.

Wata majiyar tsaro ta shaidawa AFP cewa gungun mayakan sun yi kokarin farmakar sansanin Soji da ke Patacua amma Sojin suka fi karfinsu tare da fatattakarsu ta hanyar amfani da jiragen yaki.

Tun cikin shekarar 2017 yankin Cabo Delgado na Mozambique kef ama da hare-haren ta’addanci amma kuma matsalar tsaron ta janyo hankalin Duniya ne bayanda mayakan masu ikirarin jihadi suka kwace iko da Palma tare da dakatar da aikin hakar iskar gas na dala biliyan 20.

Daruruwan mutane ne yanzu haka suka kauracewa matsugunansu daga yankin yayinda s uke gudun hijira a wasu sass ana kasar don tsira da rayukansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.