Hadarin jirgin Sojin Kenya ya hallaka mutum 10 tare da jikkata 13
Wallafawa ranar:
Rundunar sojin Kenya ta ce dakarun kasar 10 ne suka rasa rayukansu sanadiyyar hadarin da wani jirgi mai saukar angulu ya yi kusa da birnin da su a safiyar jiya alhamis.
Sanarwar ta bayyana cewa akwai wasu sojoji 13 da suka samu raunuka a wannan hadari wanda ya faru dai dai lokacin da jirgin ke kokarin sauka.
Ma’aikatar tsaron kasar da ke sanar da faruwar lamarin a safiyar yau, ta ce jirgin Sojin kirar Mi 171 E na dauke da dakarun kasar da ke dawowa daga wani horo na musammanya lokacin da aka samu tangardar sauka da misalin karfe 9 na safiyar jiya.
Sanarwar ma’aikatar da kafofin labaran kasar suka wallafa ta ce za a gudanar da bincike don gano musabbabin faduwar jirgin.
Haka zalika ta sanar da cewa yanzu haka sojoji 13 da suka samu rauni a hadarin na samun kulawar gaggawa a asibitin Soji na birnin Nairobi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu