Habasha - Tigray

Ma'aikatan MSF sun mutu a hare-haren da dakarun Habasha suka kai kan Tigray

Wasu 'yan Habasha yayin karbar tallafin abinci a garin Agula dake yankin Tigray. 8/5/2021.
Wasu 'yan Habasha yayin karbar tallafin abinci a garin Agula dake yankin Tigray. 8/5/2021. AP - Ben Curtis

Kungiyar likitoci ta duniya Médecins sans Frontières MSF, ta ce ma’aikatanta 3 da suka hada da ‘yar  Spain 1 da ‘yan Habasha 2 na daga cikin mutanen da aka kashe a harin da sojojin Habasha suka kai kan yankin Tigray mai fama da rikici a arewacin kasar ta Habasha.

Talla

Cikin sanarwar da ta fitar a baya bayan nan kungiyar ta MSF ta ce ta kasa samun  ma’aikatan ne da suka yi balaguro a  cikin wata mota a ranar alhamis da ta gabata, yayin da a safiyar Juma’a aka gano gawarwakin ma’aikatan lafiyar.

María Hernández, ‘yar kasar Spain mai shekaru 35, ta kasance daya daga cikin shuwagabanin sashin ayyukan gaggawa na kungiyar likitocin ta duniya  MSF a yankin Tigray.

Sai Yohannes Halefom Reda da Tedros Gebremariam Gebremichael, dukkaninsu 2 ‘yan kasar Habasha masu shekaru 31 a duniya, da suka kasance mataimaka da kuma direban kungiyar ta MSF.

Tun cikin watan Nuwamban bara dakarun kasar Habasha ke fafata yaki a yankin Tigray, rikicin da ya kai ga kakkabe mahukuntan yankin mai cin kwarya kwaryar gashin kansa karkashin jam’iyar Front de libération du peuple du Tigré (TPLF).

Tuni gwamnatin, Addis Ababa ta kafa kwamitin tafiyar da mulkin rikon kwarya a yankin na Tigray.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.