Senegal

Zanga-zanga kan sabuwar dokar yaki da ta'addanci ta koma tarzoma a Dakar

'Yan sandan Senegal yayin arrangama da masu zanga-zanga a birnin Dakar kan kudirin sabuwar dokar yaki da ta'addanci.
'Yan sandan Senegal yayin arrangama da masu zanga-zanga a birnin Dakar kan kudirin sabuwar dokar yaki da ta'addanci. © REUTERS/Finbarr O’Reilly

Daruruwan mutane sun yi arrangama da ‘yan sanda a Dakar babban birnin kasar Senegal, yayin zanga-zangar adawa da wani kudurin sabuwar dokar yaki da ta’addanci da shugaban kasar Macky Sall ya mikawa zauren majalisar dokoki domin tabbatar da shi a matsayin doka.

Talla

Masu zanga-zangar sun yi amfani da abubuwa daban daban ciki har da duwatsu da zummar yiwa ‘yan sanda rotse a gaban zauren majalisar dokokin ta Senegal yayin da ake tsaka da muhawara kan kudirin dokar, abinda ya sanya jami’an tsaron maida martani da barkonon tsohuwa.

‘Yan adawa na zargin shugaba Macky Sall da kokarin kafa sabuwar dokar domin yin amfani da ita wajen cin zarafinsu da sunan yaki da ta’addanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.