Afrika - Tattalin Arziki

Kashi 31 na asibitocin Afirka kawai ke samun lantarki - Bankin Afirka

Shugaban Bankin Afrika Dakta Akinwumi Adesina.
Shugaban Bankin Afrika Dakta Akinwumi Adesina. AFP/File

Shugaban Bankin Afirka Akinwumi Adesina ya ce rayukan ‘yan nahiyar ta Afirka kimanin biliyan 1 da miliyan 200 na cikin hatsari sakamakon rashin samun ingantaccen tsarin kula da lafiya, lamarin da ya kara kamari saboda annobar Korona.

Talla

Yayin jawabi a taron kwanaki 3 na shekara shekara da bankin Afirkan AFDB ke yi, Dakta Adesina, ya ce daga cikin manyan kalubalen da kasashen Afrika ke fuskanta akwai cewar, kashi 51 na asibitoci da cibiyoyin kula da lafiya kadai ke da ruwa mai tsafta da kuma ingantaccen muhalli, yayin da kashi 31 kawai na asibitocin ke samun wutar lantarki.

Shugaban Bankin Afirkan ya kuma bayyana rahoton da ya ce kasashen Afirka na sayen kashi 60 zuwa 70 na magungunan da suke amfani da su daga kasashen ketare a maimakon samarwa a cikin gida.

Yayin taron dai, hukumar gudanarwar bankin na Afirka ta cimma matsayar ware makudan kudaden da za ta yi amfani da su, wajen inganta tsarin kula da lafiya a kasashen nahiyar, ta yadda mai karfi da maras shi za su amfana ba tare da la’akari da tattalin arzikinsu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.