CHADI-SIYASA

Deby ya ce akwai yiwuwar kara wa'adin gwamnatin rikon kwarya a Chadi

Shugaba Mahamat Idriss Deby
Shugaba Mahamat Idriss Deby AFP - CHRISTOPHE PETIT TESSON

Jagoran gwamnatin mulkin sojin Chadi Janar Mahmat Deby ya bayyana cewar sakamakon rarrabuwar kawunan jama’ar kasar da kuma rashin kudaden da ake bukata domin tafiyar da shirin mika mulki ga fararen hula nan da watanni 18 da aka shirya, akwai alamun zasu bukaci tsawaita zaman majalisar mulkin sojin kasar.

Talla

Shugaban majalisar mulkin sojin ya bayyana haka ne a tattaunawar da yayi da Jaridar Jeune Afrique inda ya bayyana halin da ake ciki a Chadi da kuma kokarin da yace gwamnatin sojin kasar keyi na mayar da mulki ga gwamnatin farar hula kamar yadda suka yi alkawari.

Sai dai daya daga cikin Yan adawan kasar Ibrahim Zain Congy ya ce dama sun san za’a rina domin kuwa haka tsohon shugaban kasa Idris Deby yayi tayi wajen tsawaita mulkin sa bayan karbe iko ta hanyar amfani da karfin soji a shekarar 1990.

Congy yace Deby yayi ta alkawarin mika mulki ga fararen hula ko gabatar da dimokiradiya ga jama’ar kasar amma kuma sai yayi ta nada kan sa a matsayin zababen shugaban kasa da sunan dimokiradiya na karya.

Dan adawar yace lokacin da shugaba Deby ya rasu sai aka kawo ‘dan sa ya gaje shi ba tare da sanya hannun sojojin kasar Chadi ko kuma amfani da kundin tsarin mulkin kasar ba.

Congy wanda ya bayyana sabuwar gwamnatin mulkin Chadi ta CMT a matsayin haramcaciya yace sun san cewar shugaban ta Mahamat Deby ba zai sauka ba bayan kammala watanni 18, saboda haka zasu ci gaba da gwagwarmaya domin ceto kasar su daga mulkin kama karya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.