Habasha-Tigray

Amurka da Birtaniya na son MDD ta yi zama na musamman kan yankin Tigray

Wasu al'ummar yankin Tigray na Habasha.
Wasu al'ummar yankin Tigray na Habasha. EDUARDO SOTERAS AFP

Kasashen Amurka da Ireland da kuma Birtaniya sun bukaci gudanar da taron kwamitin sulhu na Majaisar Dinkin Duniya cikin gaggawa domin tattauna halin da ake ciki a Yankin Tigray da ke kasar Habasha, bayan da Yan Tawaye suka sake karbe iko a Mekele, babban birnin Yankin.

Talla

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito majiyar diflomasiya na cewa ana iya gudanar da taron ranar juma’a, idan Faransa wadda zata karbi shugabancin kwamitin daga ranar 1 ga watan Yuli ta amince.

Tun bayan barkewar tashin hankalin Yankin Tigray kasashen Yammacin duniya sun gaza wajen gudanar da taro akai sakamakon kin amincewar kasashen China da Rasha da kuma wasu kasashen Afirka dake kallon matsalar a matsayin ta cikin gida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.