Afrika ta Kudu - Jacob Zuma

Jacob Zuma ya sha daurin watanni 15 sakamakon rena kotu

Tsohon shugaban afrika ta Kudu, Jacob Zuma.
Tsohon shugaban afrika ta Kudu, Jacob Zuma. POOL/AFP/File

A wani hukunci  da ba a saba gani bam ai cike da tarihi, babbar kotun Afirka ta Kudu ta yanke wa tsohon shugaban kasar Jacob Zuma hukuncin zaman gidan yari na watanni 15, bayan samunsa da laifin rena kotu, biyo bayan kin bayyana a gaban masu binciken zargin rashawa da ake mai.

Talla

An shaida wa Zuma cewa ya miki kansa nan da kwanaki 5, kuma idan ya gaza yin biyayy za umurci ‘yan sanda su tisa keyarsa zuwa kurkuku.

Wannan hukunci ya gwada wa kasar ta afrika ta kudu misali, kuma abin kwatance ga nahiyar, ta wurin jefa tsohon shugaba a kurkuku sabili da kin bada hadin kai ga binciken rashawa.

yayin yannke hukuncin, alkaliyr kotun, Sisi Khampepe ta ce an samu Jacob Gedleyihlekisa zuma da laifin raina kotu, saboda haka ba wanda ya fi karfin doka.

Ana zargin Zuma mai shekaru 79 da samar da yanayi da ya bada damar na wawushe dukiyar al’umma yayin kusan shekaru 9 da ya shafe yana mulkin kasar kafin jam’iyya mai mulkin kasar ta ANC ta tilasta masa yin murabus a watan Fabrairun 2018.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.