Habasha - Tigray

Jami'an Habasha sun arce daga Tigray, gwamnati ta ayyana tsagaita wuta

Taswirar Habasha da ke nuna yankin Tigray.
Taswirar Habasha da ke nuna yankin Tigray. Aude GENET AFP

Gwamnatin Habasha ta ayyana tsagaita wuta ta kashin kanta a yankin Tigray da ke fama da rikici, biyo bayan kutsawa babban birnin yankin da ‘yan tawaye suka yi.

Talla

Mayakan ‘yan tawaye sun shiga babbaan birnin yankin da karfin tuwo, har sai da jami’an gwamnatin Habashan suka arce, lamarin da ya janyo murna da anashuwa a birnin, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito.

An jiyo wani jami’in gwamnati na cewa ‘yan tawaye sun karbe ikon birnin.

Da take sanar da matakinta, gwamnatin Habasha ta ce tsagaita wutar zai yi aiki ne har karshen damunar bana, don a samu sukunin gudanar da aikin noma da zai wadata yankin da abinci, biyo bayan kashedin da majalisar dinkin duniya ta yi cewa matsalar matsanancin yunwa na nan tafe.

A safiyar Litinin dinnan, 'yan tawayen tigray sun sha alwashin korar wadanda suka kir abokan gaba a yankin, duk da sanarwar tsagaita wuta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.