Mali-MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta yi tir da take hakkin dan adam a Mali

Jagoran mulkin Soji na Mali Kanal Assimi Goïta.
Jagoran mulkin Soji na Mali Kanal Assimi Goïta. REUTERS - FRANCIS KOKOROKO

Majalisar Dinkin Duniya ta yi tir da matakin amfani da karfin da ya wuce kima da dakarun gwamnatin kasar Mali ke yi sakamakon karuwar take hakkin bil adama da ke barazana ga fararen hula.

Talla

Shugabar Hukumar kare hakkin bil Adama Michelle Bachelet ta bukaci gwamnatin kasar da ta dinga amfani da dokokin kasa da kuma hukunta wadanda suka wuce gona da iri wajen kare lafiyar jama’a.

Kasar Mali na ci gaba da fuskantar tashin hankali sakamakon karuwar ayyukan 'yan bindiga wadanda ke kai hare hare ba tare da kaukautawa ba, abinda ya yi sanadiyyar mutuwar dubban fararen hula da jami’an tsaro.

Duk da kasancewar dubban sojojin Faransa da na Majalisar Dinkin Duniya har yanzu ana ci gaba da samun tashin hankali a cikin kasar wanda ya fadada zuwa kasashen Nijar da Burkina Faso.

Rahotanni sun ce tsakiyar kasar Mali ya zama dandalin tashin hankali a Yankin Sahel wanda ke fama da hare haren dake da nasaba da kabilanci da kuma wanda ake kaiwa akan dakarun gwamnati lokaci zuwa lokaci.

Bachelet ta bukaci gwamnatin Mali da ta tashi tsaye wajen dakile wadannan hare hare da kuma cin zarafin fararen hula wajen gudanar da bincike na gaskiya da kuma hukunta wadanda aka samu suna da hannu a ciki.

Majalisar Dinkin Duniya ta gano irin wadannan cin zarafi 617 cikin su harda kisan da yan bindiga suka yi sau 165 daga watan Janairu zuwa Yunin bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.